Shugaban tawagar Santiago yace zasu je koina a Najeriya amma banda jihohin Borno, Adamawa da Yobe sabili da dalilan tsaro.
Amma yace zasu raba masu duba zabe a duk fadin kasar domin sa ido. Santiago wanda ya gana da Janaral Buhari yace zasu yi anfani da jami'ansu domin tabbatar da ingancin zaben. Banda haka Santiago ya bada tabbacin zai gana da Shugaba Jonathan kamar yadda Sakatare Kerry na Amurka yayi.
Janaral Buhari ya sake nanata bukatar gudanar da zabe cikin lumana. Ya kuma musanta rade-radin cewa gwamnatin Jonathan ta rufe asusun da yake karbar taimakon jama'a na gudanar da zabe.
Janaral Buhari yayi wa jama'a godiya dangane da gudunmawar da suke bashi. Yace duk abun da aka bashi daga nera dari suna zuwa asusun bankinsa dake Bankin Farko ko First Bank. Yace kudin da suke aikawa suke yin anfani dasu. Yace duk kudin da ya shiga ko kwandala ba zata fita ba sai ya sa hannu. Da kudin yake yakin neman zabe.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka.