Yanzu haka an tsaurara matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba dangane da zuwan manyan yan takarar shugaban kasa, Shugaba Goodluck Jonathan na jam’iyar PDP, da kuma Janar Muhammadu Buhari.
Tuni ma,gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana yau laraba da gobe alhamis a matsayin ranakun hutu,yayin da aka kafa dokar hana fita tun daga karfe takwas na dare zuwa biyar na asuba,kana kuma aka hana yan Keke Napep ,da yan amalanke da masu saida rake,yin sana’a har na tsawon kwanaki biyu,batun da jam’iyar APC,tace bata amince ba.
Jam'iyyar APC ta bakin kakakinta a jihar Rev Pinas Padiyo, ta bada sanarwar cewa an dage zuwan Janar Buhari, kuma ba'a bayyana ranar da zai je jihar yakin neman zabe ba, duk da cewa zai yi yakin neman zabe a makwabciyar jihar Taraba a laraban nan.
Rev Padio yace jam'iyyar tana shakkar gwamnatin PDP mai mulkin jihar tana da wata manufa na bada wannan hoto, saboda idan da gaskenen suna son karrama Janar Buhari, ai da hukiumomin jihar basu hana jam'iyyar amfani da babban dandalin taro dake fadar jihar da ake kira 'Ribadu Square".
Ahalinda ake ciki kuma jam'iyyar APC a jihar Taraba, ta kammala dukkan shirye shirye domin tarbar dan takarar shugabancin kasar Janar Buhari wanda ake sa ran zai kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Laraban nan.
Ga karin bayani.