Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jinkirta Zabe Ka Iya Gurgunta Dimokradiya-inji Jam'iyyar PDP


Shugabannin Jam'iyyar APC.
Shugabannin Jam'iyyar APC.

Shugabannin jam'iyyar APC na cigaba da cewa jinkirta zabe ka iya yiwa dimokradiya karan tsaye

Yin hakan kuma ka iya zama wata dabarar wahalar da 'yan adawa da gangan domin rage masu karfi.

Ibrahim Abdulkarim mai kula da asusun tarawa Janaral Buhari kudin yakin neman zabe. Yace idan suka hakikance a dage zaben su a APC ina zasu samo kudin da zasu cigaba da yakin neman zaben. Yace nera dari- dari mutane ke basu.

Idan an kara lokacin yin zabe su ne za'a kwara. Tamkar an mayardasu baya ne. Su ko PDP suna da kudin gwamnati da suke anfani dashi. Idan aka dage zabe suna da kudin da zasu yi anfani dashi.

Banda haka ga bala'in faduwar kudin man fetur. Ina Najeriya zata iya daukar nauyin jinkirta zabe.

Idan har za'a yi zaben kan lokaci alamun nasara na ga 'yan adawa inji Sanata Hadi Sirika. Yace ranar zabe doka ce kuma babu wanda zai iya dagata cikin ikon Allah. 'Yan Najeriya ba zasu yadda ba. Su ma 'yan majalisar dattawa ba zasu yadda ba.

Shugaban matasan APC Dasuki Jalo Waziri yana kiran matasan jam'iyyar da su kaucewa tashin hankali.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG