Ganin yadda ake ta kafa alamomin kamfe din siyasar Nijeriya, musamman ma na PDP da APC, abinda ka iya kawo tashin hankali a kasar, hukumomin kasar sun haramta kafa wadannan alamomin.
Wakilinmu a Ghana Baba Yakubu Makeri ya shaida ma Aliyu Mustafa cewa yawan ‘yan Nijeriya da ke kasar ta Ghana a yanzu ya zarce miliyan daya, wannan ya sa wasu jam’iyyun siyasa ke ta kokarin tallata jam’iyyarsu a kasar. To amma y ace ba wannan ne karon farko da siyasar wata kasa ta shigo Ghana ba; ya ce ko a bara ma, sai da kampe din kasar Mali ya shigo Ghana. Game da Nijeriya kuwa, y ace har zuwa kasar Ghana wasu shugabannin siyasar Nijeriya ke yi don tallata jam’iyyarsu da kuma zawarcin masu kada kuri’a.
Ya ce lallai ‘yan Nijeriya da ke Ghana kan tafi Nijeriya su kada kuri’a a lokutan zabe. Yace tashin hankalin Boko Haram ya dada sa hukumomi da jama’a na dari-dari da ganin siyasar Nijeriya na shiga Ghana.