Wata babbar motar soja ta kai gomman mutanen da aka kwaso daga makarantar Ecole Kirkisoye ta biyu da ke shiyyar Yamai ta 5 sansanin da ake kira Camp Gamo da hukumomin Nijar suka kafa a matsayin wata mafakar wucin gadi.
Sansanin na dauke da daruruwan dakunan tamfol da aka rarraba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta ruguza gidajensu.
Hakazalika an tanadi fomfunan ruwa da makarantar firame yayin da a nan gaba za a sanya musu wutar lantarki, amma Malama Delou Ousman na cewa akwai wani hamzari ba gudu ba.
Ta ce yaransu da ke zuwa makaranta zasu fuskanci kalubalen abun hawa saboda tazarar da ke tsakanin sansanin da makarantun, don haka ya kamata gwamnati da dauki wani mataki a kai.
Yayin wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa suka bayyana jin dadinsu tare da godewa hukumomi, wasu daruruwan mutane da ke makarantar ta Kirkisoye sun ce ba su ji dadin tsarin da aka yi amfani da shi wajen tantance wadanda za a bai wa mafaka a wannan sabon sansanin ba.
Dubban mutane ne ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a fadin kasar Nijar a bana sakamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya.
Hakan ya faru ne yayin da yankunan da Kogin Kwara ya haddasa babbar barna lamarin da ya tilasta wa jama’a tarewa zuwa makarantu dabam-daban.
Sai dai kuma lura da karatowar lokacin kammala babban hutun ‘yan makaranta ya sa mahukuntan NijAr kaddamar da shirin kwashe wadannan mutanen zuwa wata sabuwar mafaka.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5