Rahotanni na bayyana cewa Trump na ci gaba da samun goyon bayan akasarin manoma da suka amfana da shirin tallafawa aikin goda da gwamnati ta samar musu.
Wakiliyar Muryar Amurka Kane Farabaugh tace baicin annobar coronavirus, batun taimako da cinikayya na cikin zukatan manoman yayin da suke shirin kada kuri’a a ranar uku ga watan Nuwamba, a fafatawar neman kujerar shugaban kasa tsakanin Trump da abokin karawarsa na Democrat Joe Biden.
Ma’aikatar aikin gona ta Amurka ta fada yayin da ake rikicin cinikayya, cewa farashin waken soya yayi kasa da kashi 35 cikin dari tsakanin 2014 da 2019, ko kafin annobar corona ta rage adadin da China ke saye.
Haka farashin masara, daya daga cikin muhimman amfanin gonar wani manomi mai suna Wendell Shuama, tayi kasa da kashi 44 cikin dari tsakanin shekarar 2014 da 2019.
Shuama ya ce bai ga wani farfadowa da aka samu ba. "Farashin ya yi muni matuka a cikin wannan shekara. A abubuwa da dama da na sayar, yayi kasa sosai fiye da abin da nake tunanin zan samu.” in ji shi.
Hakan ne yasa manoma kamar Moore da Shuaman suka ce shirin taimakawa kasuwanci da ma’aikatar aikin gona ta Amurka ta kirkiro da ke biyan manoma tun cikin shekarar 2018, yake agaza musu.
Facebook Forum