Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Filato Ta Fito Da Sabuwar Dabarar Yaki Da COVID-19


Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong

Ma'aikatar lafiya ta jahar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ta samo wata sabuwar dabarar yaki da cutar coronavirus a jihar.

Jami'ar hukumar dakile yaduwar cutuka ta jihar Matina Alex Nuwan, ta ce sabon tsarin da aka yi wa lakabi da ‘Box In’ zai taimaka wajen fadakar da jama’a muhimmancin fitowa domin yin gwajin da samun magani.

Ta ce babban makasudin sabon tsarin shi ne domin tabbatar da ana yin gwajin cutar sosai, ta yadda za'a sami gano duk inda cutar ta ke, ta kuma shiryawa tunkarar ta.

Nuwan ta ce jihar ta Filato na sahun gaba wajen kokarin gwajin cutar a Najeriya, kuma ta ce "za'a ci gaba da wannan kokarin, musamman ga mutanen da aka gano cewa sun kusanci masu dauke da cutar."

Jami'ar ta ce ko bayan gwajin ma, akan shawarci wadanda suka kusanci masu cutar da su ma su kebe kan su na wani lokaci, kafin fitowar gwajin da aka yi musu.

Rakiya Munkaila, wata jami'ar fadakar da jama'a a sha'anin kiwon lafiya a jihar, ta ce akwai hatsarin kamuwa da cutar a tsakanin masu sana'ar tuka keke-NAPEP da mafi akasari ba sa amfani da takunkumin rufe fuska kamar yadda masu acaba da babura suke yi.

Akan haka ta kara jaddada bukatar jama'a su rika bin dokokin da hukumomi suke shata wa, da suka hada da saka takunkumi, wanke hannuwa da kuma ba da tazara a tsakanin jama'a.

Alkaluman hukumar dakile cutuka ta Najeriya - NDDC, sun bayyana cewa ya zuwa yanzu, jihar ta Filato na da mutane 3,499 da suka kamu da cutar ta COVOD-19, yayin da mutane 33 suka mutu sakamakon cutar a jihar.

Ga rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG