Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamata Ya Yi Sojoji Su Koma Kan Aikinsu Na Tsaro, In Ji Gwamna Zulum


Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum.
Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umaru Zulum.

A cigaba da cece kucen da ake yi game da matsalar tsaro a Najeriya, gwamnan jahar Borno, Umara Zulum ya ce akwai bukatar sojoji su nisanci siyasa su mai da hankali kan aikinsu na tabbatar da tsaro.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kalubalanci jami'an sojin Nigeriya da su maida hankali kan yaki da ta'addanci da ke addabar kasar maimakon shiga harkokin siyasa.

Gwamnan ya bayyana hakkan ne lokacin bude wani taron babban hafsan sojan kasa na Nigeriya a garin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin Kasar.

Babban hafsan sojan kasan Nijeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce, sun samu gudanar da zabubbuka ba tare da samun wani cikas ba, musamman ma a zaben da aka gudanar a jihar Edo, ya kara da cewa Shirin “Operation Safe Conduct” da aka aiwatar lokacin zabe a jihar Edo shaida ne, kuma yana yaba wa jami’an sojan kasar.

A jawabin da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya gabatar ya fara ne da yaba wa jami’an sojan Najeriya kan yadda suke gudanar da aikinsu, ya ce, amma ya kamata jami’an sojan kasar su mayar da hankali kan yaki da ta’addanci.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG