Gwamnatin ta najeriya ta gabatar da kasafin kudin na shekara ta 2021 ne na kusan Naira tiriliyan 14, da take hasashen samu a albarkatun man fetur da kasar ta dogara da shi, akan dalar Amurka 40 akan kowace gangar man, da take hako ganga miliyan 1.86 a kowace rana.
Sha'anin tsaron kasar ya sami kason Naira biliyan 840.56 a kasafin kudin na 2021, sabanin Naira 878.4 da ya samu a kasafin kudin da ya gabata, a yayin da ma'aikatar lamurran cikin gida ta sami Naira miliyan 227.2, ma'aikatar lamurran 'yansanda kuma ta sami Naira biliyan 441.39.
Bangaren Ilimin kasar ya sami kason Naira biliyan 545.10 a kasafin kudin, inda ma'aikatar lafiya kuma aka ba ta kason Naira biliyan 380.21.
Dr. Dauda Muhammad Kontagora, wani masani tattalin arziki a Najeriya, ya ce wannan hasahe ne na abin da gwamnati za ta samu a shekara mai zuwa, wanda kuma aiwatar da shi ya ta'allaka da abin da aka samu na kudade.
Ya ce abin lura shi ne gwamnatin da yanzu haka take a shekarun ta na karshe akan mulki, ana sa ran ta aiwatar da ayuka masu amfani ga al'umma, da za su sa a tuna da ita bayan ta wuce.
To sai dai yana ganin wata kila gwamnatin za ta maida hankali ne akan karasa ayukan da ta fara.
Ga cikakken rahoton Babangida Jibril:
Facebook Forum