An Rantsar da Adama Barrow A Matsayin Shugaban Gambia

Shugaba Adama Barrow yayinda ake rantsar dashi a matsayin shugaban Gambia jiya

Jiya aka rantsar da Alhaji Adama Barrow a matsayin shugaban kasar Gambia a ofishin jakadancin kasar Gambia dake Senegal yayinda kuma sojojin kasar ta Senegal da na wasu kasashen Yammacin Afirka suka fara shiga Gambia domin su kawar da Yahya Jammeh wanda ya ki sauka cikin ruwan sanyi

Dr Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja yace rantsar da Adama Barrow ya nuna cewa shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da gaske su keyi na tabbatar cewa sun kawar da Jammeh kana Barrow ya zama shugaban kasa na halal bisa ga zabensa da 'yan kasarsa suka yi.

Abun da zai faru yanzu shi ne sojojin kasashen zasu yi masa rakiya ya shiga kasarsa ya kama mulki gadan gadan bisa tafarkin dimokradiya. A ganin Dr Kari nan da 'yan kwanaki kadan zasu fitar da Yahya Jammeh idan bai fita da kansa ba.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Dr Aliyu Idi Hong ya kalli rantsuwar da fuskar diflomasiya. Yace a duniya yau Adama Barrow shi ne shugaban kasar Gambia saboda mutanen kasar sun zabeshi kuma wa'adin Yahya Jammeh ya kare kuma an rantsar dashi a kasar Gambia ne saboda ofishin jakadancin kasa kasar ce. Haka ma ECOWAS da kungiyar Afirka AU da Majalisar Dinkin Duniya sun amince da zaben Adama Barrow.

To amma lauyan tsarin mulki Barrister Yakubu Saleh Bawa yace rantsar da Adama Barrow a wajen kasar Gambia ya sabawa tsarin mulki kana ba alkali ba ne ya rantsar dashi, shugaban lauyoyi ne ya rantsar dashi. Kamata yayi alkalin alkalan kasar Gambia ya rantsar dashi.

Amma tsohon jakadan Najeriya a kasar Sudan Ambassador Suleiman Dahiru yace bisa ga dokokin diflomasiya na duniya ofishin jakadancin Gambia a Senegal kasar Gambia ce saboda haka rantsar dashi a ofishin yayi daidai.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rantsar da Adama Barrow A Matsayin Shugaban Gambia - 2' 56"