Mai maganan Mai Fatty ya fadawa kamfanin dilancin AFP cewa a ranar sha tara ga wannan wata wa’adin shugaba Jammeh zai kare kuma a lokacin shi kuma Adama Barrow zai fara wa’adin mulkin sa. Babu abinda zai canja . A bayan da shugabanin kasashen kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS suka kasa shawo kan shugaba Jammeh da ya rungumi kadara ya sauka daga kan ragamar mulkin bayan wa’adin mulkin sa na shekaru biyar ya kare, Mr Barrow ya tafi kasar Senegal.
Ba’a tantance nan da nan abinda yasa Mr Barrow ya tafi kasar Senegal ba, to amma kafofi sun baiyana cewa a saboda rashin matakan tsaron kare shi yadda ya kamata ne yasa ya tafi kasar Senegal.
Shugaban Senegal yayi na’am da bukatar Mr Barrow ta zuwa kasar Senegal har zuwa ranar da za’a rantsar da shi.