An Kasa Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Nasarawa Da Kungiyar Kwadago

Engr. Abdullahu Sule, Gwamnan jihar Nasarawa

Kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta kasa cimma matsaya da gwamnatin Jihar kan yarjejeniya da zai kawo karshen yajin aiki da ma’aikatan Jihar ke yi.

Bayan an yi ta kai ruwa rana tsakanin ma’aikata da gwamnati kan wasu bukatu na yin karin girma, biyan albashi da sabon tsari akbashi mafi karanci na dubu talatin da sauransu, ma’aikatan suka ce ba su yadda da wani sashe na yarjejeniyar da gwamnati ba.

Sashen yana magana ne kan cewa biyan kudin karin girman zai danganta ne ga yawan kudin da gwamnatin ta samu a ko wane wata.

Shugaban kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa, Yusuf Sarki Iya ya ce sun lura cewa sa hannu a yarjejeniyar ba za ta kai ga gaci ba don haka za su ci gaba da yajin aiki.

Kwamishinan shara’a a Jihar Nasarawa Dakta Abdulkarim Abubakar Kana ya ce za su ci gaba da tattaunawa har sai sun samu daidaitu a tsakaninsu.

A halin da ake ciki dai ma’aikatun Jihar ta Nasarawa da cibiyoyin lafiya mallakar jihar za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai bangarorin biyu sun cimma matsaya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kasa Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Nasarawa Da Kungiyar Kwadago