Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Ohanaeze Ta Jaddada Muhimmancin Kasancewar Igbo A Najeriya


Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta jaddada muhimmancin kasancewar 'yan kabilar a kasar Najeriya, tare da bada goyon baya ga nesanta kansu da gwamnonin kudu maso gabashin kasar suka yi daga ayyukan haramtacciyar kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewa daga Najeriya.

A wata hira da sashen Hausa na Muryar Amurka, kakakin wannan kungiyar, Cif Alex Ogbonna, ya bayyana matsayin kungiyar akan batun ficewa ko kuma ci gaba da kasancewa a karkashin tutar Najeriya:

Ya ce, "Matsayin kungiyar Ohanaeze Ndigbo sananne. Ya ce, "mun yarda da kasancewa a hadaddiyar Najeriya guda da ke tabbatar da raba daidai da kuma adalci. Ya fi dacewa nesa ba kusa ba a kasance a wurin da ya fi sarari da dadin walwala. Ko da ma an samu hanyar dunkula Afirka ta yamma baki daya a karkashin mulkin Najeriya, hakan ya fi dace mana. Saboda haka, kasancewa a inda ya fi sarari, zai fi bunkasa harkokin mu da wanzuwar mu."

A ranar Asabar din nan da ta gabata ne gwamnonin kudu maso gabas suka gudanar da wani muhimmin taro a Inugu, babban birnin jihar Inugu, inda suka fito karara suka nesanta kansu daga fafutukar da haramtacciyar kungiyar IPOB ta ke yi, ta kafa kasar Biafra.

A taron dai, gwamnonin yankin ta bakin jagoransu, gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya Dave Umahi, sun ayyana cewa: "Mu 'yan kabilar Igbo muna sake jaddada cewa, mun dukufa ga hadaddiyar Najeriya guda a karkashin jaddamalin adalci, da daidaiton dama, da kauna, da kuma mutunta juna."

Gwamnonin dai sun kara da cewa, "Muna Allah wadai da kashe jami'an tsaro da ma kona muhimman kadarorin gwamnati, da kuma kashe farar hula a kudu maso gabas, da ma sauran yankuna. Muna kuma tir gaba daya da ayyukan 'yan aware a kudu maso gabas, da sauran wurare. Muna ayyana cewa ba ma goyon bayansu, kuma ba a madadin kudu maso gabas suke fafutukar su ba."

Kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewa daga Najeriya ta na ci gaba da tada kayar baya da kai hare hare musamman kan jami'an tsaro da jadada niyarsu ta ballewa daga Najeriya domin abinda su ka kira rashin adalci da ake nunawa kabilar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG