Gwamnonin sun kuma yi Allah wadai da hare-hare da kungiyar IPOB ke kaiwa da ya biyo bayan sake sabunta fafutukar neman shiyyar kudu ta bale dana Najeriya ta kasance kasa mai cin gashin kanta ta Biafra lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ne ya bayyana hakan a madadin sauran takwarorinsa biyo bayan ganawa da suka yi a ranar Asabar domin neman mafita ga yanayin dardar da ake ciki na rashin tsaro tare da dawo da doka da oda da zaman lafiya a yankunan su.
Gwamnonin na kudu sun dora alhakin dukannin hare-haren baya-bayan nan da aka yi ta kaiwa kan ofisoshin jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati a yankunan kudu maso gabas akan kungiyar ta IPOB.
A wata hira da ya yi da manema labarai makonni biyu da suka gabata, tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha, ya ce dattawa yankin suna yin shiru ne saboda gudun kada a kai wa iyalansu hari.
Sai gwamna Umahi ya ce babu kamshin gaskiya a cikin zarge-zargen cewa, sun yi shiru kan lamarin da ke faruwa a yankunansu yana mai cewa ba sa goyon bayan matasan da ke wannan fafutuka, ya na mai cewa, 'yan kungiyar IPOB ba su da hurumin yin magana a madadin 'yan kudu.
Haka kuma, gwamna Umahi, shugabannin yankunan kudu sun kafa kwamiti da zai shiga tsakani da matasan masu fafutukar neman balewa don fahimtar da su kan duk abin da ke ci musu tuwo a kwarya.
Daga karshe, gwamnonin sun bukaci hukumomin tsaro a yankin su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda dokar kasar ta tanadar tare da mika bukatar mambobin majalisun kasar daga yankin, su mara baya ga batun kafa ‘yan sandan jiha a aikin gyara kundin tsarin mulki da su ke aiki a kai a halin yanzu.
Idan ana iya tunawa, a shekarar 2012 ne kungiyar IPOB ta fara fafutukar balewa daga kasar inda gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana kungiyar a matsayin haramtaciyya bayan wasu taho-mu-gama da jami’an soji a yankunan kudu.