Wannan sabon gargaɗi dai an bayar da shi ne a wata tattauna da kakakin yaɗa labaran Sunday Igboho, Oluyomi Koki ya yi da manema labarai a karshen mako.
A cewarsa “su na sanar da cewa daga ranar Litinin yau, ba su son ganin ko da Bafulatani makiyayi ɗaya tal a cikin jihohin Ekiti, Lagos, Oyo, Ogun, Ondo da Osun.
"Haka kwanaki suka ba da wa'adin cewa Fulani su bar wannan yankin, don haka ina kira ga gwamnatin tarayya, da a tashi da gaggawa tun abin bai kazance ba." Alhaji Salisu ba Shankai Sarkin Fulanin Shagamu ya ce.
Ya kara da cewa, ko a kwanan nan sun kona gidaje kimanin 50 na wasu Fulani a jihar Oyo, don haka ya kamata gwamnati ta dauki matakin da ya kamata na kawo karshen tashin hankali a yankin.
A cewar Sunday Igboho idan ba su ji wannan gargadi ba, shi da kansa zai rinƙa fita yana fatattakar duk wanda ya ƙi ficewa.
Yanzu haka dai sauran al’umomin Arewa mazauna yankin sun fara kira ga gwamnatin tarayya ta hanzarta daukan matakan gaggawa na magance wannan barazana.
A cewar wasu, wannan barazana ta Sunday Igboho ba ita ya kamata ya dauka ba, kowa na da ‘yancin adawa da ta’addanci da ake zargin wasu Fulani nayi, amma shi ba hukuma bane don, dole gwamnatin Najeriya ta shigo cikin lamarin da gaggawa.
Wannan barazana akan Fulani dai ba shi ne na farko ba daga Igbohon da yanzu ake wa kallon dan fafutuka a yankin na Yarbawa ba.
A kwanakin baya, an zarge shi da jagorantar kai hare-hare akan yankunan da Fulani ke zaune da ya haifar da hasarar rayukan mutane da dabbobi da kuma na dukiyoyin Fulani.
Tuni dai rundunonin ‘yan sandan jihohin yankin Yarbawa baki daya suka fitar da gargadi ga masu neman ta da husaMa da su guji yin hakan.
Yanzu dai jama'a na ci gaba da sa ido domin ganin matakin da gwamnatin Najeriya za ta dauka na magance wannan matsala tun kafin wankin hula ya kai ta dare.
Saurari rahoton cikin sauti daga Babangida Jibril: