Hukumomin shara'a na Amurka sun kama wani mutum ‘dan jihar Utah, da ake zargin yana da alaka da wasu wasikun da aka aikawa shugaban ‘kasa da ma’aikatar tsaro ta Pentagon.
WASHINGTON D.C. —
Mutumin mai suna William Clyde Allen, mazaunin birnin Logan na jihar Utah, an kama shine jiya Laraba ana zarginsa da aikawa da wasiku masu dake dauke da wani iri na wata bishiya da ake samun gubar ricin daga cikinta.
Daya daga cikin wasikun dai an rubutata ne zuwa ga shugaban Amurka, Donald Trump.
Wasiku biyu kuma an aikasu ne zuwa ma’aikatar tsaro ta Pentagon, daya zuwa ga sakataren tsaro Jim Mattis, dayar kuma zuwa ga hafsan hafsoshin sojin ruwa Admiral John Richardson.
Ita dai gubar "Ricin" aba ce mai hatsari wacce idan aka hadiye ta ko aka shake ta, ko kuma aka yi wa mutum allura da ita, nan take take iya hallaka mutum a cikin wa'adin sa'oi 48 kacal.