Ana alakanta wani ambulan dake dauke da adireshin shugaba Donald Trump na Amurka dake dauke da gubar sinadarin ricin da wadansu wasiku biyu da aka karbe a ma’aikatar tsaro ta Pentagon.
Sanarwar da ma’akatar ayyukan tsaron ciki ta fitar ta tabbatar da samun wasikar da ake da alamar tambaya a kai da aka rubutawa shugaban Trump ranar daya ga watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha takwas. Sanarwar ta kara da cewa, ba a fadar shugaban kasa ta White House aka karbi wasikar ba, kuma wasikar bata shiga fadar White House ba.”
Jami’an ma’aikatar tsaron sun shaidawa Muryar Amurka cewa, an sami gubar risin a jikin dukan wasikun da aka aika ma’aikatar tsaro daya da sunan sakataren tsaro Jim Mattis, daya kuma zuwa ga shugaban ayyukan rundunar mayakan sama Admiral John Richardson.
An kai wasikun ofishin Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI jiya Talata domin kara bincike, bisa ga cewar kakakin ma’aikatar tsaro Kanar Rob Manning.
Wasikun sun isa ofishin rarraba wasiku na ma’aikatar tsaro dake wajen ginin Pentagon ranar Litinin. Jami’an kare ma’aikatar suka gano gubar lokacin da suke bincike wasikun, saboda haka wasikun basu shiga ginin ma’aikatar tsaro ba, inji jami’an.
Ana dai samun gubar ricin ne a wani irin wake. Idan aka shaketa ko aka ci ko kuma aka yiwa mutum allura da ita bayan an sarrafa ta, tana iya kashe mutum a cikin sa’oi arba’in da takwas. Bisa ga cewar cibiyar kare yaduwar cututaka ta Amurka, gubar ricin bata da magani.
Facebook Forum