Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cece Kuce Diplomasiyya Tsakanin Kasashen Duniya akan Iran


Yayin da shuwagabanni kasashen a wajen baban taron majalissar dinki duniya a Birnin New York, suke kokarin nazirin zargin da shugaban Amurka Donald Trump yayi cewa China na kokarin yin shisshigi a zaben Kasar Amurka da za’a gudanar a watan gobe, China da kakkausan harshe ta musanta wannan zargin.

A yayi da cece kucen ke kara tsamari tsakanin Amurka da sauran kasashen da suka sa hannu gameda makomar yarjejeniyar Nukiliyar Iran ta 2015 a taron majalissa na bana, Amurka na kokarin kakaba wa kasar Tehran ta kunkumi. A lokacin da jagoranci taron kwamitin sulhu a ranar laraba.

Shugaba Trump ya maida hankalin shi a kasar Iran inda ya zarge ta da laifin haddasa rikice rikice da kashe kashe. Ana cikin haka ne kuma, Prime Ministan Isira’ila Benjamin Netanyahu ya zargi Iran da laifin cewa tana da wata masana’antar boye makaman nukuliya na sirri a birnin Tehran

Mr Netanyahu yace Iran bata yi watsi da burin ta na kera makaman nukiliya ba. Prime Ministan yayi wanan furucin ne a wajen baban taron Majalisar Dinkin Duniya, harma ya nuna wa Majalisar hotuna da taswirar ginin da yake zargin Iran tana boye makamai a cikin sa.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif yayi watsi da zargin na Mr Nitanyahu. Yace burin Mr Natanyahu shine boye ainihin gaskiyar cewa Isira’ila itace babar barazana a yankin. Iran ta sha musunta cewa tana kokarin kera makaman nukiliya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG