Shugaba Trump ya yi hasashen cewa, "Wannan muhimmiyar yarjajjeniyar za ta samar da mankudan kudi da kuma ayyukan yi su kwararowa cikin Amurka da kuma kasashen Arewacin Amurka."
Bayan tattaunawa mai zurfi da aka yi a makare, gab da wa'adin da masu tattaunawar su ka gindaya ma kansu, Amurka da Canada sun ba da sanarwar cimma yarjajjeniya, wadda ta amince cewa yarjajjeniya mai kunshe da canje-canje, wadda ta shafi kasashe ukun, ta maye gurbin ta da wato NAFTA, wadda aka yi amfani da ita na tsawon shekaru 25.
Yarjajjeniyar ta cinakayyar da ta kai dala tiriliyan 1.2 a shekara guda, an tsara ta ne kan, abin da Trump ya kira, "adalci da kuma sakayya." Trump ya ce cimma yarjajjeniyar ya biyo bayan takaddama tsakaninsa da Shugabannin kasashen Mexico da Canada, wato Enrique Pena Nieto da Justin Trudeau.
Facebook Forum