An Kafa Dokar Ta Baci A Kasar Habasha

Hailemariam Desalegn

Majalisar ministocin kasar Habasha ta ayyana dokar ta baci ta watanni uku a kasar, wadda ta kama aiki nan take.

An fitar da sanarwar ne a kafofin watsa labarai kwana daya bayanda Firai minista Hailemariam Desalegn ya sanar da yin murabus.

Wata sanarwar gwamnati tace an ayyana dokar ta bacin ne domin kiyaye doka da oda da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa. Sanarwar ta kuma ce an yanke wannan shawarar ne sabili da kawo karshen fadan kabilanci da kashe kashe da lalata kaddarori da aka fuskanta a kasar.

Ethiopia ta yi fama da tarzomar kin jinin gwamnati cikin shekarun da suka shige, da kira a gudanar da zabe mai sahihanci a kuma dama da dukan kabilun kasar. Hadakar kungiyar EPRDF mai mulki ita ce ke rike da dukan kujerun majalisar kasar.

A yunkurin kwantar da hankali, cikin wannan makon gwamnati ta saki sama da fursunoni dari bakwai da aka kama yayin zanga zangar kin jinin gwamnati da kuma lokacin da aka kafa dokar ta baci a baya. Wadanda aka saki sun hada da fitattun shugabannin hamayya da kuma wani fitaccen dan jarida Eskinder Nega, wanda yake yawan kushewa gwamnati.