Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Hauren Somaliya Da Ke Libya Sun Ki Koma wa Gida


Wasu daga cikin bakin haure 'yan Afirka a birnin Tripoli na Libya, Maris 22, 2017.
Wasu daga cikin bakin haure 'yan Afirka a birnin Tripoli na Libya, Maris 22, 2017.

Aksarin bakin hauren Somaliya da ke kokarin tsallaka teku ta kasar Libya domin zuwa nahiyar turai, sun ki komawa gida, bayan da gwamnatin kasarsu ta tura wata tawaga domin mayar da su gida.

Yunkurin da gwamnatin Somaliya ke yi na kwashe ‘yan kasarta da ke Libya, ya fuskanci turjiya, bayan da tawagar da kasar ta tura, ta gaza shawo kan bakin hauren Somaliya masu kokarin tsallaka teku zuwa nahiyar turai, kan su guji wannan hanya mai cike hadari su koma gida.

Bakin hauren Somaliyan, sun fada wa, mambobin tawagar gwamnatin kasarsu cewa, sun sha bakar wahala wajen zuwa kasar ta Libya daga Somaliya, saboda haka, suna ganin ba su da asara.

Tawagar jami’an gwamnatin ta Somaliya, ta ce ga dukkan alamu, ‘yan kasarta sun riga sun kuduri aniyar yin wannan tafiya ta teku, domin danganawa da kan iyakokin nahiyar turai.

A ranar Litinin din da ta gabata, mambobin tawagar gwamnatin ta Somaliya suka isa birnin Tripoli, sun kuma ce sun kai ziyara wuraren da ake rike da bakin, sannan sun hadu da wasudaga cikinsu a ofishin jakadancin Somaliyan.

Amma kuma duk da haka, mutane 11 ne kacal suka nuna sha’awar za su koma Somaliya.

Kiyasi ya nuna cewa, akalla ‘yan kasar ta Somaliya 5,000 zuwa 6,000 ne suka yi kaura zuwa Libya da nufin tsallaka teku, a cewar jami’ai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG