Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Sojojin Habasha Dauke da Makamai Sun Kutsa cikin Kasar Somalia


Sojojin Ethiopia suna sintiri
Sojojin Ethiopia suna sintiri

Kimanin motoci talatin dauke da sojojin kasar Habasha suka ketara zuwa cikin kasar Somalia da zummar taimakawa sojojin Somalai a yakin da su keyi da mayakan al-Shabab

Daruruwan sojojin Habasha dauke da manyan makamai, sun ketara zuwa cikin kasar Somaliya, kuma rahotanni na cewa sun je su taimaka ma rundunar sojojin gwamnatin Somaliya ne, a yakin da take da mayakan al-Shabab.

Mazauna garin Dolow na kan iyaka a yankin Gedo na kasar Somaliya, sun ce sun ga akalla motoci 30 dauke da dakarun kasar Habasha, suna ketarawa zuwa cikin kasar ta Somaliya da yammacin jiya Talata.

Shaidun da su ka yi magana da Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka bisa sharadin a sakaya sunayensu, sun yi kiyasin cewa sojojin kasar Habasha kimanin 1,000 ne su ka shiga kasar ta Somaliya.

Wani mazaunin garin ya ce motocin na sojoji ne da kuma na daukar kaya, wadanda aka girke bindigogi masu sarrafa kansu a samansu.

Akwai dubban sojojin Habasha a kasar Somaliya a matsayin wani bangare na rundunar gamayyar sojojin Afrika ta AMUSOM, da aka girke don su yaki al-Shabab.

Hukumomin nahiyar da Muryar Amurka ta tuntuba jiya Laraba sun tabbatar da shigar sojojin Habasha din a cikin Somalia.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG