Tawagar dake karkashin jagorancin kasashen rennn Faransa ya isa Nijar a ci gaba da kokarin dinke barakar dake tsakanin bangarorin 'yan siyasar kasar ta Nijar. Yanzu dai an kusa kwashe shekara guda inda jam'iyyun adawa da 'yan babu ruwanmu basu halarci taron majalisar CNDP ba.
A wannan ziyara jami'an sun gana da shugabannin jam'iyyun 'yan babu ruwanmu kana washe gari suka gana da jam'iyyu masu rinjaye. Daga bisani kuma sun gana da 'yan adawa a wani kokarin kawo karshen kiki-kakar da ta dabaibaye ayyukan kwamitin sasanta rikicin siyasar wato CNDP.
Amma 'yan adawa sun yi watsi da kasancewa a taron CNDP kamar yadda Annabo Sumaila jigo a jam'iyyar 'yan adawa ta FRDDR ya bayyana. A cewarsa ita CNDP ta na da kura-kurai da yawa, kuma muddin ba'a gyarasu ba, to ba zasu halarci duk wani taro da ta kira ba. Inji shi bangarori uku ne suke cikin CNDP da suka hada da 'yan adawa da PNDS da 'yan babu ruwanmu.
Amma yau sai CNDP ta zama kamar ta bangare daya ne, wato ta bangaren PNDS mai mulki kadai. Jagoran tawagar Robel Dosul bai so yin wani daogon bayanin abin dake tafe dasu ba, saboda a cewarsa ya zo ne ya karanci yanayin da ake ciki saboda haka sai magana ta kai karshe yake da bakin magana. To saidai su 'yan FRDDR sun ce abu daya ne zai kawo sulhu idan an koma kan gaskiya.
A saurari rahoton Souley Barma don karin bayani.
Facebook Forum