Firai Ministan Ethiophia ko kuma Habasha, ya ba da sanarwar cewa zai yi murabus a bisa abin da ya kira a matsayin kokarin ci gaba da gyara tare da kawo sauki a siyasar kasar da ke cikin halin ha’ulai.
Da yake magana a gidan Talabijin na kasar,a yau Alhamis, Hailemariam Desalegn, ya ce, ya mika takardarsa ta barin aiki a matsayin sa na Firai Minista da kuma shugaban Jam’iyyar da ke mulki ta EPRDF Coalition ta kawance.
Hailemariam ya ce bukatar samar da gyaran wanda bai bayyana ta yazo ne a lokacin da tashe-tashen hankula suka yi kamari a kasar.
Mutane da dama sun rasa muhallansu wasu gidajensu sun lalace, wanda za su iya zama illa ga saka hannun jari saboda rikice-rikice da suka addabi kasar.
Facebook Forum