Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Dokar Ta Baci a Kasar Habasha


Siraj Fegessa Ministan tsaron Habasha
Siraj Fegessa Ministan tsaron Habasha

A kasar Habasha ko Ethiopia an dage dokar ta-bacin da aka saka tun shekarar da ta gabata, biyo bayan karin samun zaman lafiya.

Majalisar Dokokin kasar Ethiopia ta dage dokar ta bacin da aka saka a kasar tun shekarar da ta gabata, biyo bayan kwashe watanni ana gudanar da zanga-zangar da tayi sanadiyar rayuka.

Yau Juma’a ne ‘yan Majalisun suka yi wani zama na musamman, inda suka amincewa ‘dage dokar ta bacin bayan da suka saurari jawabin Ministan tsaron kasar Siraj Fegessa, wanda shine ke shugabancin rundunar ma’aikatan tsaron da aka dorawa hakkin tabattar da ana aiki da dokar ta-bacin.

A rahotan da ya gabatar, Fegessa ya ce zaman lafiya da tsaron kasar ya inganta, duk da cewa har yanzu akwai matsalolin tsaro jifa-jifa a wasu bangare na kasar.

An dai kafa dokar ta bacin ne a Habasha tun ranar 9 ga watan Oktobar shekara ta 2016, bayan da aka samu tashin hankali a babban birnin kasar Addis Ababa biyo bayan wasu aiyukkan raya birnin da aka soma, wanda kuma ya juye ya koma zanga-zangar rashin ‘kin jinin gwamnati saboda manufofinta na siyasa da keta hakkin bil Adama.

Sama da mutane 600 ne aka kashe a tashin hankalin, yayinda aka kama mutane fiye da 21,000. Ministan tsaron kasar ya ce har yanzu akwai mutane 8,000 a daure da ake zarginsu da aikata laifuka lokacin da ake tashin hankalin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG