WASHINGTON, D.C - Masu zanga-zangar dai sun yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu tare da kona tayoyi a kan tituna, yayin da jami'an tsaro su kuma suka harba hayaki mai sa hawaye, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Wannan dai shi ne zagaye na uku na zanga-zangar adawa na masu kin gwamnati da 'yan adawa suka kira a wannan watan.
'Yan sanda sun kama akalla mutane 300 a fadin kasar, ciki har da manyan 'yan adawa tara, a cewar ma'aikatar cikin gida da kuma lauyan 'yan adawa.
Hakan ya sa aka kai ga rufe makarantu a Nairobi babban birnin kasar, birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa da Kisumu, birni na uku mafi girma a kasar. Babban birnin na Nairobi ya kasance babu kowa, duk an watse, inda aka rufe kasuwanni da dama, yayin da 'yan sanda suka kafa shingayen binciken ababen hawa a kan hanyoyin da ke zuwa fadar shugaban kasa, na William Ruto.
An zabi Shugaba Ruto ne dai a watan Agustan da ya gabata, inda ya yi alkawarin kare muradun talakawa, to amma farashin kayayyakin masarufi ya tashi a karkashin gwamnatinsa kuma a watan da ya gabata gwamnatinsa ta zartas da karin haraji.
Gwamnati ta ce ana bukatar haraji ne kan man fetur da gidaje don taimakawa wajen magance karuwar biyan basussuka da kuma samar da hanyoyin samar da ayyukan yi.
Wani mai zanga-zangar a birnin Mombasa wanda ya bayyana sunansa da Eric kawai, Eric, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a lokacin da yake zuba ruwa a fuskarsa domin ya wanke hayaki mai sa hawaye cewa, "Wannan gwamnati tana taka dokar kundin tsarin mulkin kasar ne ta hanyar zaluntar mu yayin da muke kokarin tabbatar da tsarin mulki daya ta hanyar zanga-zangar lumana.”
-Reuters