Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ilawa Sun Yi Jerin Gwanon Nuna Adawa Da Shirin Gwamnati Na Yin Garambawul Ga Tsarin Shari’a


Jerin gwanon Isra'ilawa masu adawa da garambawul ga tsarin Shari’a
Jerin gwanon Isra'ilawa masu adawa da garambawul ga tsarin Shari’a

Masu zanga-zanga a Isra’ila sun toshe manyan tituna tare da kutsawa cikin kasuwar hada-hadar hannayen jari , yayin da ‘yan majalisar dokoki ke shirin amincewa da daya daga cikin kudurorin dokar shari’a na Firai minista Benjamin Netanyahu da ake takaddama a kai.

Mutane da dama ne suka shiga cikin kasuwa hannayen jari ta Tel Aviv, suna jefar da takardun banki na bogi a matsayin alamomin cin hanci da rashawa.

Likitoci sun ce wata mota ta buge wata mata a kan babbar hanya kuma taji rauni. Haka kuma wani mai zanga-zanga a tsakiyar Isra'ila ya samu munanan raunuka sakamakon bugun da ya yi da gudu, ko da yake 'yan sanda sun ce mai yiwuwa hatsarin mota ne.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

Dubun dubatar ‘yan Isra’ila masu adawa da shirin gwamnatin Isra’ila na yin garambawul ga tsarin shari’a tare da kwace mulki daga hannun kotun kolin kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar.

Masu zanga -zangar sun kuma toshe hanyoyi tare da kawo koma baya a harkokin yau da kullum a duk fadin kasar.

Mutane sun daure kansu a gaban Ma'aikatar Tsaro a ranar 'Ranar Resistance' don nuna adawa da sake fasalin shari'ar Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, a Tel Aviv, 18 ga Yuli, 2023.

Mutane sun ɗaure kansu a gaban Ma'aikatar Tsaro a ranar 'Ranar Resistance' don nuna adawa da sake fasalin shari'ar Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, a Tel Aviv, 18 ga Yuli, 2023.
Mutane sun ɗaure kansu a gaban Ma'aikatar Tsaro a ranar 'Ranar Resistance' don nuna adawa da sake fasalin shari'ar Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, a Tel Aviv, 18 ga Yuli, 2023.

Yunkurin sauye-sauyen, da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin hana ‘yancin cin gashin kai na kotu, sannan a cewar Netanyahu matsayin daidaita sassan gwamnati, ya haifar da rikicin tsarin mulki na tsawon rabin shekara da yasa Amurka damuwa kan kawance ‘yan adawar kasar masu ra’ayin rikau.

~ Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG