An Gano Sinadirin Cyanide A Gawawwakin Wasu 'Yan Vietnam da Amurkawa A Otal 'Din Bangkok - ‘Yan Sanda

Binciken Cyanide

Hukumomin kasar Thailand sun bayyana a yau Laraba cewar, binciken farko da aka gudanar akan musabbabin mutuwar gawa ya nuna cewar akwai burbushin sinadarin cyanide a jinin wasu ‘yan vietnam 6 da baki Amurkawa a otel din “Central Bangkok Luxury”

Ana kuma kyautata zaton daya daga cikin mutanen ne ya sanyawa sauran guba sakamakon lalacewar wata harkar kasuwanci.

A jiya Talata aka gano gawawwakin mutanen a otel din Grand Hyatt Erawan dake Bangkok, wani fitaccen ginin dake babbar mahada a tsakiyar birnin mai cike da hada-hadar manyan shaguna da gine-ginen gwamnati da tashoshin ababen hawa na haya.

An yiwa mutanen 6 ganin karshe ne lokacin da aka kai abinci dakin da suke da daren ranar litinin.

Ma’aikaciyar otel din ta ga mace guda data karbi abincin, kuma hotunan kyamarorin tsaro sun nuna yadda sauran mutanen suka rika hallara daya bayan daya daga bisani.

Babu wasu bakin na daban, ba’a ga kowa yana barin wurin ba kuma kofar dakin ta kasance a rufe.

Wata ma’aikaciyar otel din ce ta gano gawawwakin da maraicen ranar talata bayan da suka gaza sakin dakin.

Shugaban sashen binciken kwakwaf na rundunar ‘yan sandan kasar Thailand, Laftanar Janar Trairong Piwpan, ya bayyana cewar an samu burbushin sinadarin cyanide a jikin kofuna da flas-flas da ‘yan sanda suka samu a dakin.

Daga bisani sakamakon binciken musabbabin mutuwar gawa da aka gudanar a asibitin Chulalongkorn na birnin Bangkok ya tabbatar da hakan.

A jawabinsa ga manema labarai, shugaban sashen binciken likitanci na kwakwaf a asibitin koyarwa na jami’ar Chulalongkorn, Kornkiat Vongpaisarnsin, yace an samu sinadarin cyanide a jinin gawawwakin 6, kuma hotunan sassan jikin da aka dauka sun nuna cewar babu wata alama tayin amfani da karfi akan gawawwakin, abinda ya kara karfafa hasashen da aka yi na yin amfani da guba.

-AP