Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar ke cewa, zata hada hannu da masu ruwa da tsaki a bangaren kula da ayyukan hajji a Najeriya, domin daukan matakan shawo kan matsalolin da aka fuskanta a bana.
Tun kimanin makoni biyu da suka gabata ne hukumar alhazan ta jihar Kano tayi shelar cewa, dukkanin maniyyatan da ba su sami sukunin sauke farali a bana ba, bayan biyan kudin kujerar aikin hajji, su garzaya shalkwatar hukumar domin a dawo musu da kudaden su.
A zantawa da Muryar Amurka, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, sakataren zartarwa na hukumar alhazai ta jihar Kano, ya ce aikin dawo da kudaden ya shafi rukunin jama’a guda uku ne, “akwai wadanda suka biya kudin kujera kuma suka sami biza da sauran takardun tafiya kasa mai tsarki, amma saboda tangardar jigila daga kamfanin jiragen sama na Azman ba su sauke farali ba."
Rukuni na biyu shine wadanda suka yi adashen gata da hukumar alhazai, amma bayan ayyana hakikanin kudin kujera ba su iya cika kudaden ba, rukuni na uku shine alhazan da suka je aikin hajji, amma ba su cika kwanakin da aka kayyade zasu yi ba, saboda an kiyasta cewa, alhazan Kano zasu yi kwanaki 35 ne a kasa mai tsarki, amma galibin su kwanaki 30-31 suka yi, don haka za’a dawo musu da kudaden abinci da na sauran dawainiya na ragowar kwanakin.”
Kimanin maniyyata dubu ne daga jihar Kano ba su samu zuwa aikin hajjin ba, saboda tangarda da aka fuskanta daga kamfanin jirgin sama na Azman, wadda shine hukumar alhazai ta Najeriya ta baiwa kwangilar jigilar alhazan jihar.
Yanzu haka dai wasu daga cikin maniyyatan sun fara karbar kudaden su daga hukumar alhazai ta jihar Kano.
Umar Ibrahim daga karamar hukumar Kunci ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ya karbi kudaden sa naira miliyan 2 da rabi, da ya biya domin zuwa aikin hajjin bana 2022.
Shima Malam Ishaq Aminu Tijjani wanda ya biya wa matar abokin sa, naira miliyan biyu da rabi, ya ce hukumar alhazan ta Kano ta maido masa da kudaden.
Duk da cewa, an shiga mako na biyu da shelar dawo da kudaden ga alhazan, amma ya zuwa yanzu kalilan daga cikin su suka nuna sha’awar karbar kudaden.
A bayaninsa, Sakataren hukumar alhazan ta Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya ce wasu daga cikin maniyyatan na cike takardun amincewa da ci gaba da barin kudaden nasu a hannun hukumar zuwa aikin hajji na badi.
Bisa ga cewarsa, hukumar alhazan ta Kano ta koyi darrusa da dama daga kalubalen da suka fuskanta a bana, kuma suna kokarin daukar matakan da suka dace tare da sauran masu ruwa da tsaki domin magance afkuwar su a gaba.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5