Jimillar kamfanonin jiragen sama uku ne hukumar alhazan Najeriya ta amince suyi jigilar alhazan kasar dubu 43 zuwa kasa mai tsarki domin aikin hajjin bana.
Kamfanonin sun hada da kamfanin Fly Nass da MaxAir da kuma Azman Air.
Yayin da aka kaddamar da jigilar alhazan a makon jiya, rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa, wasu daga cikin jihohi da suka hada da jihar Kano sun bayyana kin amincewar su da kamfanin jiragen sama na Azman.
Alhaji Abba Mohammed Danbatta dake zaman sakataren zartarwa na hukumar alhazan Kano ya ce a ra’ayinsa, kamfanonin jiragen da hukumar Haji ta Kano ta yi aiki da su shekaru hudu jere bada wata tangarda ba, sune ya kamata su ci gaba da aiki da su.
Sai dai Alhaji Lawan Sulaiman dake zaman babban manajan aikace-aikace na kamfanin Azman Air ya ce tuni suka fara jigilar alhazan da hukumar kula da ayyukan hajjin ta Najeriya ta amince su yi safarar su zuwa Saudiyya su fiye da dubu 7 a jihohi daban daban na Najeriya daga ciki akwai na jihar Kano da adadin su ya zarce dubu biyu.
Sashen Hausa ya tuntubi kakakin hukumar alhazai ta Najeriya Hajiya Fatima Usara ta kuma ce bata da wata masaniya dangane da hukuncin hukumar na baiwa kamfanin Azman jigilar alhazan jihar Kano.
Rahotanni sun ce da yammacin yau ne aka tsara gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai kai wata ziyara ofishin shiyyar Kano na hukumar alhazai ta kasa, ziyarar da wasu ke alakantawa da kokarin tausasa hukumar ta amince da bukatar gwamnatin jihar Kano ta kwace jigilar alhazan jihar daga kamfanin jiragen sama na Azman Air, duk kuwa da cewa, kamfanin mamallakin dan asalin jihar Kano ne.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari: