Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Maniyyata Daga Jihar Kano Na Fargaban Ba Za Su Samu Damar Zuwa Aikin Hajji Ba


Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON)
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON)

Yayin da hukumomin Saudiyya suka kara wa Najeriya kwana biyu domin ta sami sukunin jigilar alhazanta zuwa kasa mai tsarki, har yanzu maniyyata aikin hajji daga kasar musamman jihar Kano na bayyana shakku akan yuwuwar kwashesu zuwa Saudiyya la’akari da yadda jigilar ke tafiyar hawainiya.

KANO, NIGERIA - Da fari dai an ayyana Litinin 4 ga watan Yuli a matsayin ranar da hukumomin Saudiyya zasu rufe kafofin shiga kasar don tunkarar aikin Hajji gadan-gadan, amma wata sanarwa da hukumar kula da ayyukan Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta fitar da yammacin ranar Litinin ta tabbatar da karin wa’adin wanda ake sa ran kamfanonin da ke jigilar alhazan na Najeriya zasu kammala aikin su.

Sai dai duk da wannan kari maniyyata daga Najeriya musamman na jihar Kano, na bayyana shakku da fargaba kan yuwuwar zuwansu kasa mai tsarki. Baba Bala Sheka, na daga cikin maniyyatan, ya ce suna nan suna jira amma har yanzu basu ga jirgin Azman ba.

Mata Maniyyata aikin Hajjin da ke jira a sansanin alhazai na Kano su ma sun bayyana damuwa game da halin da suka shiga, kamar yadda Zulaiha Buhari ta fada.

Kimanin maniyyata dari tara da doriya daga cikin maniyyatan jihar Kano dubu biyu da ashirin da tara ne suka isa kasa mai tsarki, wanda kamfanin jiragen Azman ne ke kwangilar jigilarsu. Sai dai duk da haka kamfanin na Azman ya bada tabbacin kwashe dukkan maniyyatan, kamar yadda Alhaji Nuradeen Aliyu jami’in kula da ayyukan Hajji na kamfanin ya bayyana.

Sai dai duk da haka hukumar alhazai ta jihar Kano ta ce ta nemi agaji daga hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya dangane da wannan batu, kamar yadda Abba Mohammed Danbatta sakataren zartarwa na hukumar ya bayyana.

Hakan dai na faruwa ne a daidai lokacin da Malaman bita ke ci gaba da fadakar da maniyyata game da aikace-aikacen Hajji.

Fiye da maniyyata dubu arba’in da hudu daga Najeriya ake sa ran zasu sauke farali a bana.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG