Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hajji: Har Yanzu Maniyyatan Kano Da Yawa Na Jira


Wasu daga cikin maniyyatan da ke jira
Wasu daga cikin maniyyatan da ke jira

Yayin da sa’oi kalilan ya rage wa’adin Karin kwanaki biyu da hukumomin Saudiyya suka baiwa Najeriya domin kammala kwashe alhazanta zuwa kasa mai tsarki, har yanzu fiye da kasha 50% na maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Kano na dakon jiragen da zasuyi jigilar su zuwa Jidda. Sai dai hukumar alhazai ta jihar Kano ta alakanta lamarin da tilasta mata aikin da kamfanin jrgin sama na Azman Air maimakon kamfanin Max Air.

Maniyyata aikin hajjin mazan su da mata wadanda ke cikin yanayi na damuwa saboda zaman rashin tabbas, sun zargi hukumar alhazai ta Kano da kamfanin jiragen sama a Azman da-ma hukumar kula da ayyukan aikin hajji ta Najeriya da rashin jika alkawari.

Galibin su dai sun biya kudaden kujerun su na aikin hajji tun a shekara ta 2020 wadda bai gudana ba saboda barkewar cutar Corona a duniya.

Bags belonging to some intending pilgrims
Bags belonging to some intending pilgrims

Wasu daga cikin maniyyatan da suka kwashe kwanaki 6 kenan a sansanin alhazi na Kano.

A halin yanzu dai akwai wani rukuni na maniyyatan da suka kwashe kwanaki biyu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano suna dakon zuwan jirgin Azman.

Sai dai sakataren zartarwa na hukumar alhazi ta jihar Kano Alhaji Abba Muhammad Danbatta ya alakanta wannan yanayi da matakin hukumar kula da ayyukan hajji ta Najeriya na kakaba musu kamfanin Azman maimakon kamfanin Max Air da suka fi kaunar suyi aiki dashi.

Amma duk da haka sakataren alhazan na Kano ya bayya fata da yakinin cewa, za’a kwashe dukkanin maniyyatan gabanin wa’adin Karin lokaci da hukumomin saudiyya suka baiwa Najeriya ya kare.

A baya dai hukumar kula da ayyukan hajji ta Najeriya tace kamfanin flynass na kasar saudiyya ne zai kai agajin gaggawa domin taimakawwa a kwashe alhazan na Kano, amma ya zuwa lokacin hada wannan rahoto zancen ya zama lami.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG