Amurka Za Ta Ba Burkina Faso Dala Miliyan 55 Don Gudanar Da Ayyukan Jin-kai

Shugaban Amurka Joe Biden, Fadar White House a Washington, Mayu 02, 2024.

Amurka za ta bayar da kusan dala miliyan 55 don magance matsalar jin-kai a Burkina Faso, in ji jami’ar bayar da agaji ta Amurka Samantha Power a ranar Alhamis, a cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya gani.

WASHINGTON, D. C. - Taimakon zai magance bukatun abinci na gaggawa da abinci mai gina jiki da kuma sauran tallafi, in ji Power.

Kuɗaɗen za su kawo jimillar taimakon gaggawa na Hukumar Raya Ƙasa ta Amurka ga Burkina Faso zuwa kusan dala miliyan 158 tun farkon kasafin kuɗin shekarar 2023.

A cikin sanarwar da Power ta fitar ta ce, "rikicin da ke kara tabarbarewa a Burkina Faso na faruwa a cikin al'ummomin da aka raba duniya da jin duriyarsu.” Power ta ce cikin sanarwar.

"Tashe-tashen hankula da hare-hare kan fararen hula da tabarbarewar ababen more rayuwa sun haifar da tarwatsa jama'a tare da dakile muhimman ayyuka, wadanda suka bar ‘yan Burkina Faso kusan miliyan 6.3, wato kusan kashi uku na al'ummar kasar cikin bukatar agajin gaggawa a bana."

-Reuters