Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ba Yankin Sahel Tallafin Sama Da Dala Miliyan 150


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Amurka ta ce za ta ba yankin Sahel da ke Afirka wani sabon tallafin kudi na dala miliyan 152 domin tallafawa yankin wanda ya kasance daya daga cikin yankunan da ke fama da tarin rigingimu a duniya.

Wakilin Amurka na musamman mai kula da yankin na Sahel, Peter Pham ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan wata ziyara da ya kai yammacin Afirka, inda ya dangana da kasashen Mauritania da Jamhuriyar Nijar.

Tallafin zai je ga al’umomin da ke cikin mawuyacin hali ne a Burkina Faso, Mali, Mauritania da kuma Jamhuriyar Nijar.

Shi dai yankin na Sahel na fama da matsalolin masu ikrarin jihadi da na sauyin yanayi da kuma ringingimu na siyasa.

“Sama da mutum miliyan 2.5 sun fice a gidajensu, a yankin na Sahel, miliyan 3.3 na bukatar agaji da tsaro, Amurka na mai alfaharin zama babbar mai ba da gudunmowa ga yankin.” In ji Pham yayin wani taron da aka yi inda aka bayyana tallafin wanda cibiyar Wislon Center Africa ta shirya

Wadannan kudade sun fito ne daga sashen kula da yawan al’uma da ‘yan gudun hijra da masu yin kaura a ma’aikatar harkokin wajen Amurka da kuma hukumar raya kasashe masu tasowa da ba da agaji.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG