Gwamnatocin Burtaniya da Amurka sunce sun damu matuka da rahotannin kisan gillar da sojojin Burkina Faso suka yi wa fararen hula a karshen watan Fabrairu.
Rahoton Human Rights Watch na baya-bayan nan ya yi cikakken bayani kan yadda aka kashe akalla fararen hula 223 da suka hada da yara 56 a kauyukan Nondin da Soro na lardin Yatenga na Burkina Faso. Lamarin da ya sa suka yi kira ga hukumomin rikon kwarya da su binciki wadannan kashe-kashen da aka yi da su tare da hukunta wadanda suka aikata laifi.
Sanarwar ta ce kasashen biyu na mika ta'aziyyarsu ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin kasar Burkina Faso a 'yan watannin baya-bayan nan da suka hada da Kiristoci da Musulmi da kungiyoyin 'yan ta'adda suka kashe a wuraren ibadarsu, da kuma sojojin da aka kashe.
Ta ci gaba da cewa suna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Burkina Faso da su mutunta hakkin dan adam, kuma su bi dokokin jin kai na kasa da kasa kamar yadda ya dace.
Hanya daya tilo da za a magance matsalar ta'addanci ita ce fadada shugabanci nagari bisa bin doka da oda, mutunta hakkin dan Adam, da inganta hadin kan al'umma.
Burtaniya da Amurka sun ce suna adawa da dakatarwar da aka yi wa kafafen yada labarai, da suka hada da Muryar Amurka da BBC, da katange shafin yanar gizon Human Rights Watch, da kuma hana duk kafafen yada labarai ba da rahoto kan labaransu.
Wannan kira ya zo daidai da ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya a ranar 3 ga Mayu, wanda ke tunatar da mu cewa al'ummomi suna bukatar karfafawa, ba barazana ba, ta hanyar baiwa jama'a damar bayyana ra'ayoyinsu. Dole ne a bar kafofin watsa labarai masu 'yanci da masu zaman kansu damar gudanar da bincike da bayar da rahoto na gaskiya ba tare da tsoron ramuwar gayya ba.
Burtaniya da Amurka sun karkare sanarwar da kira da babbar murya ga Majalisar Koli ta Sadarwa ta Burkina Faso (CSC) da ta sake yin la'akari da dakatar da kafafen yada labaran da ta yi.
Dandalin Mu Tattauna