Ita Pyongyang tace ta shiga fargaba ne dalilin wasu haloli da Amurka take nunawa a kan shirinta na kera makaman nukiliya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kiran kasashen duniya a yau Asabar da su tsaurara matakan takunkumi a kan wannan kasar da ta kebe kanta. Kalama nashi sun biyo bayan wani kashedi da Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewa duk da takunkumin da aka dorawa shirin nukiliyar Korea ta Arewa, tana ci gaba da kerawa.
Pompeo ya nanata muhimmancin tabbatar da matsin lambar diflomaisya da na tattalin arzikin domin cimma wannan manufa ta wargaza shirin nukiliyar wanda ita Korea ta Arewa din ta amince a baya.
A wani martani, ministan harkokin wajen Korea ta Arewa Ri Yong Ho yace, kasarsa ta yi tsayin daka kuma ta himmantu wurin aiwatar da shirin wargaza makaman nukiliyar.