Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Kokarin Yiwa Zaben Amurka Katsalandan


Dan Coats, daraktan hukumar dake tattara bayanan sirri ta Amurka
Dan Coats, daraktan hukumar dake tattara bayanan sirri ta Amurka

A wani lamari da ba a saba gani ba, manyan shugabanni a fannin tsaron Amurka, sun bayyana a dakin ganawa da manema labarai da ke Fadar White, inda suka nuna damuwa kan yunkurin da Rasha da wasu ke yi na yin katsalandan a zaben tsakiyar wa’adin da ke tafe.

Shugabannin na tsaro sun kuma yi kira jama’a su kwantar da hankulansu domin ana daukan tsauraran matakan kariya wajen dakile wannan yunkuri.

“Muna ci gaba da yin karo da sakonnin da Rasha ke amfani da su wajen raunana zaben da raba kan Amurkawa,” inji Darektan hukumar tattara bayanann sirri, Dan Coats, yana mai cewa yana sane ba “Rasha ce kadai kasa da ke yunkurin yin katsalanda a fagen siyasar kasar ba.”

Coats ya kara da cewa, shugaba Trump ya “ba su umurnin cewa su dauki batun na katsalandan a matsayin abu mafi muhimmanci a aikinsu.”

Daga cikin wadanda suka hallara a wajen taron na jiya Alhamis, har da Darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Christopher Wray, da Sakatariyar hukumar tsaron cikin gida ta Homeland Security, Kirstjen Nielsen da kuma darektan hukumar tsaron kasa, Janar Paul Nakasone.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG