Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barnar Wutar Daji A California Ta Kara Muni


Irin barnar da wutar ta yi a jihar California
Irin barnar da wutar ta yi a jihar California

Adadin barnar da wutar daji ta yi a California ya kara muni saboda sama da gidaje 1000 ne suka kone krmus lamarin da ya sa gwamnan jihar Jerry Brown ya yi alkawarin bada duka abun da ake bukata domin a shawo kan wutar da ta fi muni a tarihin jihar

Adadin barnar da wutar daji mafi muni tayi a jihar Califonia ya karu daga jiya Laraba, domin sama da gidaje dubu daya ne suka kone kurmus yayin da wasu dari biyu suka samu illa.

Yayin da yan kwana-kwana ke kokarin kashe wutan a kusa da birnin Redding dake kilomita 600 daga arewa maso gabashin birnin San Fransisco, Gwamna Jerry Brown ya shaidawa manema labarai cewa zai aike da dukkan wani abu da ake bukata domin samun nasarar kashe wannan wutan.

Sai dai kuma wata daya da samar da kasafin kudin wannan shekarar, tui har jihar Califonia ta kashe dala miliyan 130, kashi daya daga cikin hudu na kasafin kudin ta na shekara.

Maaikatar kula da gandun daji da kare gobara ya fada cewa wasu gine-gine da suka kai 440 ciki harda runbunan adana kaya na cikin wadanda suka kone.

Wannan gobarar dai ita ce ta 6 mafi muni a tarihin jihar

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG