Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Yada Labaran Fadar White House Ta Kare Shugaba Trump


Sarah Huckabee Sanders sakatariyar yada labaran fadar White House
Sarah Huckabee Sanders sakatariyar yada labaran fadar White House

Sarah Hukabee Sanders sakatariyar yada labaran Fadar White House ta kare shugaba Trump bisa furucin da ya yi na cewa atoni janar din kasar ya dakatar da bincike na musamman da Robert Mueller yake yi akan zanrgin cewa Rasha ta yiwa zaben 2016 katsalandan

Sakatariyar yada labarai ta fadar White House Serah Huckabee Sanders tace ko kusa Shugaban Amurka Donald Trump baya kawo cikas ko kadan ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka akan kasar Rasha na game da katsalandan din da ake tuhumar tayi a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 wanda ya kawo shugaban kan karagar mulki.

Maimako ma yana fada ne da wannan.

Sanders tana magana ne da manema labarai a jiya Laraba, bayan da shugaba Trump ya bayyana bukatar kawo karshen wannan binciken na musamman.

Trump dai ya ce ne binciken da Robert Mueller ya kwashe watanni 14 yana yi akan alakar Rasha da yakin neman zaben sa wani al’amari ne mara kyau.

Trump yaci gaba da cewa a shafin sa na Twitter ya kamata babban mai shara’a na kasa, Jeff Session wanda yake shine alhakin kula da dokokin kasa ke hannun sa ya dakatar da wannan bita da kullin haka nan kafin yaci gaba da “zubar da martabar kasar mu”.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG