Shugaban rundunar sojin ruwan Amurka, Admiral John Richardson, ya ce suna ci gaba da sa ido, kan atisayen da sojin ruwan Iran ke yi a Tekun Persia, kuma za su tabbatar da cewa ba a samu cikas ba wajen samun walwalar zirga-zirgar jiragen ruwa a muhimman hanyoyin da ke wannan yankin tekun, wanda Iran ta ke barazanar za ta rufe.
Rundunar sojin ruwan Amurka, kan kare ka’idojin zirga-zirga akan tekun, wadanda suke ba da damar ratsawa ta wannan mashigi.
Yankin na Tekun Persia, wanda ke gabar gabashin tekun a yankin mashigin Hormuz, na daya daga cikin muhimman hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasashe a duniya.
Kwanan nan, rundunar sojin juyin-juya halin kasar ta Iran ta IRGC, ta yi barazanar rufe wannan mashigi.
Wani jami’in Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa, manya-manyan jiragen ruwan Iran sun hallara a wannan yanki domin gudanar da atisayen soji.
Facebook Forum