Pakistan tayi watsi da zargin da Amurka ke yi mata na cewa wai ita Pakistan din tankade da rairaya take idan anzo maganar kungiyoyin ‘yan ta’addan da take kai wa farmaki, sannan kuma wai tana barin kungiyoyin ‘yantawaye suna anfani da kasarta wajen kaiwa makwapciyarta Afghanistan hare-hare.
Mashawarci kan harakokin tsaro na Amurka H.R. McMaster ne yake gayawa wata tashar TV ta Amurka cewa gwamnatin Donald Trump na son kasashe irinsu Pakistan su daina bada wurare da kayan aiki ga kungiyoyin ta’addanci irins na Taliban da Haqqani.
Sai dai kuma kakakin ma’aikatar harakokin wajen Pakistan, Nafees Zakaria ya gayawa VOA cewa ba haka abin yake ba, yace Pakistan bata nuna banbanci wajen fattatakar ‘yan ta’adda ko wadanne iri ne, ya kuma ce kasarshi bata taba ba, kuma ba zata taba barin wata kungiyar mayaka tayi anfani da kasarta ba wajen kai wa swata kasa farmaki.
Daman Amurka da Afghanistan sun dade suna zargin cewa Pakistan na yakar masu jayayya da gwamnatin kasar, kuma tana fattakarsu da kyau, amma kuma ta kyale kungiyoyin ta’addanci na kasa-da-kasa suna cin karensu, ba babbaka.