Kwamitin sulhu na MDD baki dayansa ya amince da kudurin da Amurka ta gabatar wanda ya zai hana Koriya Ta Arewa morar dala milyan dubu daya na kudaden shiga a shekara data take amfani da su wajen tafiyar da shirin Nukiliya da makamai masu linzami a kasar.
Matakin zai hana kasar samun sulusin kudaden shiga da take samu dala milyan dubu uku duk shekara daga kayayyaki da take sayarwa a ketare. Kudurin ya auna sassa hudu da suka hada da tama da karafa, da wasu sinadarai da ake samun Uranium, da kuma abinci alabarkatun ruwa.
Jakadiyar Amurka a MDD Niki Haley tace, Amurka tana "dauka kuma zata ci gaba da daukar matakai kare kanta da kawayenta" daga barazanar KTA, wadda tace "tana kara kara habaka cikin hanzari cike da hadari."
Wadannan matakan suna zaman martani kan gwajin makamai masu linzami da zasu iya kaiwa Amurka da turai, da kasar ta yi cikin watan Yuli.
Facebook Forum