Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Cinikayya Ta Kasashen Latin Mercosur Ta Dakatar Vezuela Sai Illa Masha'Allahu.


Kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan wani taro da minisotcin kasashen waje na kungiyar suka yi a Brazil.

Kasashen Latin Amurka dake cikin wata kungiyar cinikayya da ake kira Mercosur, sun dakatar Venezuela ci gaba da kasancewa cikinta. Wannan mataki yana zuwa ne sa'o'i bayan da sabuwar majalisar da aka azawa nauyin rubuta sabon tsarin mulki a Venezuelan,ta kori babban mai gabatar da kara ta kasar.

Bayan wani taro a birnin Sao Paulo cibiyar cinikayya ta Brazil, ministan harkokin wajen kasar Aloysio Ferreira ya gayawa manem alabarai cewa "ku daina haka! kashe kashen ya isa haka,danniyar da ake yi ta isa haka. Yana da wuya a ci gaba da gallazawa al'uma haka."

Dakatarwa ta sai illa masha'allahu ce. Vezezuele ta shiga kungiyar ne a shekara ta 2012, kuma an taba dakatar d a ita a baya, saboda ta gaza sauke nauyi da ya wajaba a kanta.

Ahalinda ake ciki kuma,sabuwar majalisar rubuta tsarin mulkin wacce take cike da magoya bayan shugaba Maduro, ta amince da korar babbar mai gabatar da kara a kasar Luisa Ortega. Tuni kuma ta sa aka rantsar da magajinta Tarek Sa'ab.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG