A karshen taron da jagabbanin kasashen nahiyar suka kamala a birnin Sao Paulo bna kasar Brazil ne, ministan harakokin Brazil din, Aloysio Ferreira yake gayawa manema labarai cewa sun gaji da ganin shirmen dake faruwa a kasar ta Venezuela da ya hada da kashe-kashe da danne hakkokin jama’ar kasar.
Wannan dakatarwa da aka yi wa Venezuela ba’a saka mata ranar karewa ba, kuma wannan ba shine karo na farko da aka taba dakatar da kasar ba: an taba dakatar da ita a can baya saboda ta kasa cika alkawurran da ta dauka wa kungiyar.
A jiya Assabar ne dai wannan sabuwar majalisar tsarin mulkin ta Venezuela wacce aksarin wakilanta duk cikakkun magoya bayan shugaban Venezuela din, Nicolas Maduro ne suka cire ita lauyar, Luisa Ortega kuma suka nada Tarek William Saab ya maye gurbinta.
A da shi Saab shine babban jami’in kula da hakkokin jama’a na Venezuela amma Amurka ta sha zarginsa a can baya da cewa ya kasa yin wannan aikin na kare hakkokin jama’ar.
Bayanda aka cire ta ne kuma gungun sojan Venezuela suka toshe wa Luisa Ortega hanyar shiga opishinta.
A halin yanzu kuma…madugun jam’iyyar masu ra’ayin gurguzu na Venezuela din, Disodado Cabello yace an kai wani harin da yace na “ta’adanci” ne akan wani barikin soja dake garin Valencia.
Sai dai kuma a sakon da ya aika kan dandalinsa na twitter, Cabello, wanda shima magoyin bayan shugaba Maduro ne, yace soja sun shawo kan al’amarin.
Wannan lamarin ya biyo ne bayan wani faifan bidiyo da aka watsa inda aka ga wasu mayaka a cikin kayan sarki na soja kuma dauke da bindigogi, suna kaddamarda bore akan gwamnatin shugaba Maduro a jihar Carabobo inda garin Valencia yake.
Facebook Forum