Stephane Dujarric, mai magana da yawun Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya fadi a wata takardar bayani cewa Sakatare-Janar din na MDD na abin da ya kira, "maraba da duk wata hanya ta sake tattaunawa da Amurka kan yarjajjeniyar ta Paris."
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fadi jiya Jumma'a cewa za ta cigaba da kasancewa cikin duk wata harka ta tattaunawa kan batun sauyin yanayi a matakin kasa da kasa, yayin da Amurka ke bin matakin janyewa sannu a hankali daga yarjajjeniyar, wanda zai dau shekaru uku.
Ma'aikatar ta ce a shirye Shugaba Donald Trump ya ke ya sake hawa kan teburin shawara kan batun yarjajjeniyar ta Paris muddun AMurka ta ga sharuddan da su ka gamshe ta, su ka gamshi harkokin kasuwancinta su ka kuma gamshi jama'arta.
Trump ya bayyana niyyarsa ta ficewa daga yarjajjeniyar ta batun yanayi tun a cikin watan Yuni, ya na mai bayyana yarjajjeniyar da abin da ya kira "matukar kwara ga mutanen Amurka." Ya ce yarjajjeniyar na iya sa Amurka bayar da dinbin kudi baya ga nakksa harkar kasuwancin Amurka da ayyukan yi da makamashi da kuma harkokin kere-kere.
Facebook Forum