A yau Juma’a Majalisar nazarin kundin tsarin mulkin kasar Venezuela ta soma taronta na farko a zauren Majalisar dake birnin Caracas, duk da korafin kasashen duniya da kuma zanga-zangar ‘yan masu adawa.
Zaman‘Yan Majalisar su 545 da aka zaba su sake nazarin kudin tsarin mulkin kasar Venezuela zai iya janyo takun saka tsakanin shugaban kasa Nicolas Maduro da ‘yan jam’iyyar adawa, wadanda suka ce ba a yi adalci a yadda aka zabo wakilan.
Wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, tace Amurka ba ta amince da nadin ‘yan Majalisar ba, ta kara da cewa babu inganci a zaben tunda bai samu kulawar masu nazarin zaben na kasa-da-kasa ba.
Nauert, ta ce Amurka na kallon Majalisar ne a matsayin gungun wasu da aka zaba domin su taimakawa Maduro wajen ci gaba da gudanar da mulkin kama karya, wanda batanci ne ga akidar dimokaradiyya.
Facebook Forum