Amurka ta ce tana ci gaba da nuna matsin lamba ga Isra’ila kan batun kare wuraren da ake gudanar da ayyukan jin-kai a Gaza, kwana guda bayan wani harin da Isra’ila ta kai a wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya, inda Falasdinawan da aka raba da muhallansu suke fakewa, wanda ya kashe mutum 18, ciki har da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya su shida.
A wurin wani taron manema labarai da ya gudana a Warsaw, babban birnin kasar Poland, Sakataran Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce, “Muna da bukatar ganin an kare wuraren da ake gudanar da ayyukan jin-kai, kuma wannan wani abu ne da muke ci gaba da jadadda wa Isira’ila.”
Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya ci gaba da cewa, “a halin da ake ciki kuma, muna ci gaba da ganin kungiyar Hamas ta fake a ciki, tana karbewa da kuma amfani da wadannan wuraren da suke gudanar da ayyukanta da kuma da ci gaba yin barazana, ko shakka babu, ya kamata a daina, domin wadannan ayyukan suna jefa fararen hula cikin hadari.”
Har ila yau, ya ce harin ya mayar da hannun agogo baya, inda ya sake jaddada muhimmancin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta” don dakatar da yakin Isira’ila da mayakan Hamas, wanda yanzu yake cikin wata na 12.