Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila Ya Kashe Ma'aikatan Lafiya A Lebanon


Lebanon Israel Palestinians
Lebanon Israel Palestinians

Sanarwar ta ma'aikatar lafiya ta kasar ta kara da cewa, "sakamakon hare-haren na Isra'ila, an kashe ma'aikatan jinya 25 daga tawagar motocin daukar marasa lafiya daban-daban, tare da ma'aikatan lafiya biyu, sannan ma'aikatan jinya da ma'aikatan lafiya 94 sun jikkata."

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta fada a jiya Assabar cewa ma'aikatan jinya uku ne suka mutu, wasu biyu kuma suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai a lokacin da suke kokarin kashe wuta a garin Faroun da ke kudancin kasar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce “Sojojin Isra'ila sun kai hari kan wata tawagar jami'an tsaro na farin kaya na kasar Lebanon, a lokacin da suke kokarin kashe wutar da ta tashi sakamakon hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta kai da jiragen sama.

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa dakarun ta sun kai hari tare da fatattakar 'yan ta'adda na kungiyar ta'addanci ta Amal da ke aiki a cikin wani sansanin soji na kungiyar Hizbullah a yankin Faroun da ke kudancin kasar Lebanon.

Firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya yi Allah-wadai da harin da cewa ya saba wa dokokin kasa-da-kasa, ya kuma ba da sanarwar wani taron gaggawa a gobe Litinin, tare da jakadun kasashen Yammaci da kungiyoyin kasa-da-kasa, domin magance tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da yi.

Sanarwar ta ma'aikatar lafiya ta kasar ta kara da cewa, "sakamakon hare-haren na Isra'ila, an kashe ma'aikatan jinya 25 daga tawagar motocin daukar marasa lafiya daban-daban, tare da ma'aikatan lafiya biyu, sannan ma'aikatan jinya da ma'aikatan lafiya 94 sun jikkata."

Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce ta harba wani rukunin makamai masu linzami domin mai da martani ga harin na Faroun, inda ta auna wata shelkwatar sojin Isra'ila, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG