Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bukaci Isra'ila, Hamas Su Tsagaita Bude Wuta


Gaza's Shifa hospital emergency department reopens after repair from Israeli offensive damage
Gaza's Shifa hospital emergency department reopens after repair from Israeli offensive damage

Kakakin ma'aikatar wajen Amurka Mathew Miller, ya ce Lokaci yayi da ya kamata a kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bayan da sojojin Isra’ila suka gano gawarwakin wasu mutane 6 cikin wadanda ake garkuwa da su a Gaza a karshen mako.

Amurka jiya Talata ta yi kira da kakkausar murya ga Isra’ila da Hamas da su cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin da yake neman shiga wata na 11 a Gaza, sannan a sako sauran mutanen da mayakan Hamas ke garkuwa da su.

Har yanzu akwai mutane da dama da ake garkuwa da su, wadanad suke jira a kulla yarjejeniya don a mai da su gida. Lokaci ne da ya kamata a kammala yarjejeniyar, a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Mathew Miller, abin da ya fada wa manema labarai bayan da sojojin Isra’ila suka gano gawarwakin wasu 6 cikin wadanda ake garkuwa da su a karshen mako, wadanda Hamas ta harbe su har lahira a hanyar karkashin kasa a birnin Rafa dake kudancin Gaza.

'Yan Isra’ila ba za su iya ci gaba da jira ba kuma. Suma Falasdinawan da suke shan bakin ukuba sakamakon wannan yakin ba zasu iya kara jira ba. Kazalika duniya ma ba zata iya jira ba, in ji Miller.

Yace a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa Amurka zata yi aiki da masu shiga tsakani na Misra da Qatar domin kara kaimi don a kai ga kulla wannan yarjejeniyar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG