Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa, Jamus Da Birtaniya Sun Amince Da Kiran Tsagaita Wuta A Gaza


Khan Younis a kudancin southern Gaza
Khan Younis a kudancin southern Gaza

Shugabannin kasashen Faransa, Jamus da Birtaniya sun amince da kiran tsagaita wuta a Gaza, da mayar da dumbin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su da kuma kai agajin kayayyakin jin-kai ba tare da wata tangarda ba.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a ranar Litinin, shugabannin sun amince da sabon yunkurin da kasashen Amurka, Qatar da Masar suka yi na kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas da aka kwashe watanni 10 ana yi.

Khan Younis, Gaza Strip, Aug. 11, 2024.
Khan Younis, Gaza Strip, Aug. 11, 2024.

Masu shiga tsakani sun shafe watanni suna kokarin ganin bangarorin su amince da wani shiri mai matakai uku wanda Hamas za ta saki sauran mutanen da aka kama a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba domin musanya wa Falasdinawa da Isra'ila ke daure a gidan yari sannan Isra'ila za ta janye daga Gaza.

"Dole ne a kawo karshen fada a yanzu, kuma dole ne a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su da Hamas ke tsare da su. Al'ummar Gaza na bukatar kayayyakin agaji cikin gaggawa ba tare da wata tangarda ba,." In ji sanarwar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da firaministan Birtaniya Keir Starmer ne suka sanya wa sanarwar hannu.

Olaf Scholz
Olaf Scholz
Firaiminista na Birtaniya Keir Starmer.
Firaiminista na Birtaniya Keir Starmer.

Sanarwar ta kuma yi kira ga Iran da kawayenta da su kaurace wa duk wani harin ramuwar gayya da zai kara ruruta wutar rikicin yankin bayan kashe wasu manyan mayakan shugabannin biyu a watan jiya a Beirut da Tehran.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG